Babban taro kan Boko Haram a birnin Yamai | Labarai | DW | 20.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban taro kan Boko Haram a birnin Yamai

Taron a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar an kira shi ne kan batun yaki da kungiyar Boko Haram, wanda ya samu halartar kasashe 13 na Afirka da kuma wasu kasashen da ba na Afirka ba.

Kasashen dai sun hada da kasar Jamus, Canada, China, Spain, Amirka, Faransa, da kuma Birtaniya, yayin da a bengaran kasashen na Afirka aka samu halartar ministocin harkokin wajan kasashen Benin, Kamarun, EKwatoriyal Gini, Najeriya, Chadi da kuma Nijar a wannan taron. An kuma samu halartar manyan kungiyoyi na kasashen Afirka, kamar su CBLT ta kasashen da ke kula da tafkin Chadi, da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, da kungiyar CEN-SAD ta kasashen yankin Sahara, da kungiyar Tarayyar Afirka, da Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kungiyar kasashen Larabawa ta OIC.

Da ya ke magana yayin buda wannan zaman taro, Ministan harkokin wajan kasar Nijar Mohamed Bazoum, ya ce sanin kowa ne dai yanayin tsaro a Tarayyar Najeriya da kuma yankin tafkin Chadi, ya yi mummunar tabarbarewa, musammanma dangane da kama wannan birni mai mahimmanci na Baga a farkon wannan wata, ya nuna yadda 'yan kungiyar ke da karfin makammai.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman