1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hafsan sojin Aljeriya yace Bouteflika ya sauka

Abdullahi Tanko Bala
March 26, 2019

Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Algeria ya bukaci amfani da sashe na 102 na kundin tsarin mulkin kasar wajen sauke shugaba Abdulaziz Bouteflika tare da baiyana cewa bashi da koshin lafiyar da zai iya gudanar da mulki

https://p.dw.com/p/3FhA4
Algerien Algier Proteste gegen Präsident Bouteflika
Hoto: Reuters/R. Boudina

Bayan tsawon wata guda ana ta zanga zangar adawa da shugabancin Bouteflika wanda ya shafe shekaru ashirin a karagar mulki, babban hafsan sojin Aljeriya Ahmed Gaid Sala yace masalahar rikicin siyasar na kunshe a sashe na 102 na kundin tsarin mulkin kasar.

"Masalaha wadda za ta kai ga sulhunta wannan takaddama wadda kuma za ta biya bukatun jama'ar Algeria sannan mafita da za ta tabbatar da martabar kundin tsarin mulki da 'yancin cin gashin kai kasar ita ce wadda kowa zai aminta da ita da kuma dukkan bangarori. Wannan masalaha kuwa ita ce tanadin da sashe na 102 na kundin tsarin mulki ya kunsa."


A karkashin wannan doka dai ana bukatar amincewar kashi biyu cikin kashi uku na 'yan majalisar dokoki domin baiyana cewa shugaban kasar bai zai iya gudanar da mulki ba saboda rashin koshin lafiya.

Shugaba Bouteflika mai shekaru 82 a duniya ya dade yana amfani da keken guragu bayan larurar shanyewar barin jiki da ya samu a shekarar 2013 kuma ba kasafai yake fitowa a bainar jama'a ba. An sha fitar da shi zuwa kasashen Faransa da Switzerland domin neman magani.