1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babatun shugaban kasa ne ya jawo rikicin Nijar

Abdoulaye Mamane AmadouFebruary 13, 2015

A jamhuriyar Nijar kawancen jam’iyyun adawar kasar na zargin shugaban kasar da kasancewa umul’aba isin barkewar matsalar tsaro da ya fara addabar kasar.

https://p.dw.com/p/1EbVk
Präsidenten von Niger und Benin Mahamadou Issoufou Yayi Boni
Hoto: Mahaman Kanta

► A yayin wata sanarwa da kawancen adawar ya fitar, jim kadan bayan wata sanarwar da bangaren masu mulki ya yi, jam'iyyun adawar suka zargi shugaban kasa da yawan babatu da kalaman kan yaki, a duk inda ya kasance a kasashen duniya.

"Kai kana shugaban kasar da ita ce ta karshe a duniya, amma baka iya shuru, duk lokacin da ka yi magana in akwai matsala kai ne za ka sa baki ka tono bala'i ka kawo cikin kasar ka" Wannan shi ne kalalaman Malam Isuofou Tambura kakakin kawancen jam'iyyun adawa, da yake zayyana wasu daga cikin zarge-zargen da kawancen adawar ke yi wa shugaban kasar Nijar Mouhamadou Issoufou.

Mahamane Ousmane 1995 Präsident Niger
Hoto: picture-alliance/dpa

Wadannan zazzafan kalaman na 'yan adawar na zuwa ne 'yan sa'o'i, bayan yarda da amincewar da 'yan adawar kasar suka yi na tura dakarun tsaron Nijar a kawancen rundunar sojan, da aka kafa domin yaki da kungiyar Boko Haram, 'yan adawar sun ce tuni dai mai faruwa ta faruwa, matakin karshe da ya kamata shine gwamnatin da ta kara karfafa matakan tsaro tare da bai wa jami'an tsaron kasar ta Nijar damar samun wadatattun makamai, domin tun karar ya'yan kungiyar a duk inda suke.

Tambura yakara da "Duk kayan yaki dake fadar shugaban kasa wadannan kayan aikin ba na shi bane na kasa ne, ana nemansu a fagen daga, ya kamata ya bari soja su dauki kayan aiki su tafi Allah ya kiyaye su, su kare kasar mu muna goyon bayan jami'an tsaro na Nijar ne ai ba na shugaban kasa ne ba. Kenan muna goyon bayan su dari bisa dari, muna goyon bayansu. Muna fatan a samu kwanciyar hankali a cikin kasarmu da cikin jihohinmu duka da kuma cikin yankin Diffa.

Niger Niamey Gefängnis Revolte
Hoto: STR/AFP/Getty Images

A wani mataki na nuna godiya dai kawancen jam'iyyun dake mulki, a wata sanarwa sun jinjinawa 'yan adawar kasar, to amma sai dai kawancen ya mayar da martani kan kalaman da 'yan adawar suke yi, na shigar da zarge-zarge ga shugaban kasar ta Mouhamadou Issoufou. Malam Iro Sani sakataren yada labaran jam'iyyar PNDS Tarayya ne mai mulki.

"Kafin a kawo wa Nijar hari, Kamaru anka kawo wa hari, shi shugaban kasar mi ya ce koko don ya yi shurutai ne suka kai mai hari. Kara ma ka yi magana domin a farga kafin abin ya faru, tun da manufa ce da mutane su ka sakawa gaba ba, makawa sai sun yi karama ka yi magana. Mu bamu son siyasa ta shiga a cikin wannan al'amari, kuma su 'yan adawa sun nuna mana a majalisa da babu siyasa a cikin wannan batu, saboda hakan mu bar tsayawa muna Indo-Ina Ai. A cikin wannan batun mu dunguma gaba daya, mu dunguma har mu fidda Jaki daga duma. In yaso shi kenan a komo a yi siyasar. Yau in kasar nan ta rikice da yaki ,wane ne zai tsaya ya yi siyasa"

Yanzu hakan dai rahotanni na cewar ana ci-gaba da samun lafawar kura sannu a hankali a yankin na Diffa, sakamakon hare-haren da mayakan kungiyar suka kai wa garuruwa da dama, da suke yankin. Inda dokar ta-bacin da gwamnatin ta kafa ke kara bai wa jami'an tsaron kasar, damar gudanar da bincike, domin zakulo wadanda ake ganin na da nasaba da 'yan kungiyar.