1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a rusa majalisar dokoki ba a Nijar

August 23, 2013

Jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a Nijar ta bayyana cewa ba ta rasa rinjaye a majalisar dokoki ba duk da matakin da jam'iyyar Lumana Afrika ta dauka na raba gari da ita.

https://p.dw.com/p/19VR6
Hoto: DW

"Mun yi bakin ciki da ficewar da Lumana ta yi daga cikin wannan tafiya tamu ta MRN. Muna nan a kan bukarmu ta su zo a yi tafiya tare..." Wasu daga cikin muhimman kalamai da suke kunshe ke nan a cikin sanarwar da jam'iyyar PNDS Tarayya ta fitar a matsayin amsa ga matakin da takwarta ta Lumana Afrika ta dauka na raba gari da su a cikin tafiyar da milki . Ita dai PNDS Tarayya ta nesanta kanta daga duk wani zargin da ke bayyanata a matsayin dalilin lalacewar wannan kawance. Ko da shi ma Kalla Moutari daya daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar PNSD Tarayya sai da ya shaida wa 'yan jarida cewa sun yi iya kokarinsu.

"Mun yi kiransu su canza ra'ayi, mun yi lallabarsu, mutane da dama sun je wajansu hatta ma firaminista da kanshi ya dauki kafa ya je gidan Hamma domin ban magana amma duk ba ta yi ba. Kuma shekaru biyu dai muna tare da su kuma ana nade-nade kasarnan kowa ya ganemu ba abun da ba mu ka yi ma Lumana."

Mahamadou Issoufou
Jam'iyyar PNDS ta shugaba Issoufou na fuskantar kalubaleHoto: picture alliance/dpa

Batun rusa majalisar Nijar ba ta taso ba

Yanzu haka 'yan Nijar da dama na ganin ballewar jam'iyyar ta Lumana a marsayin wata babbar barazana ga makomar gwamnatin firaminista Birji Rafini da ka iya faduwa idan har Lumanar ta hade da bangaran 'yan adawa na yanzu. To amma a cikin sanarwar da ta fitar jam'iyyar ta PNDS Tarayya ta ce ba ta da wata fargaba, kuma ma magoya bayanta su kwantar da hankalinsu domin har yanzu ta na da rinjaye a majalissar dokokin kasar ta Nijar.

"Muna tabbatar wa da jama'a na kasa cewa hankalinsu ya kwanta. Wanann ficewa da Lumana ta yi kar ya kawo masu razana saboda gwamnati na da cikakken goyan baya na 'yan majalisa wanda zai ba ta damar yin mulkin kasar nan domin abokan tafiyarmu na Groupe Parlementaire ANDP su na nan tare da mu. Abokan tafiyarmu na Democrate suna nan tare da mu. Akwai ma wasu 'yan majalisa na jam'iyyu daban daban wadanda suka fitar da sanarwar cewa suna tare da mu. kenan babu fargaba."

PNDS na ci-gaba da zawarcin Lumana Afrika

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, rukunin 'yan majalisar
dokoki 25 na jam'iyyar Lumana Afrika ya ce yana goyan bayan matakin da uwar jam'iyyar ta dauka na raba gari da gwamnati. To amma kuma ministoci ukku daga cikin bakawi na jam'iyyar Lumana Afrika ne su ka halarci taron majalisar ministocin da ya wakana a ranar jumma'a. Akan wanan ne mu ka tambaya Honnorable Sale Hassan na jam'iyyar ta Lumana ko yaya su ke kallon wannan mataki na wadannan ministoci 'ya'yan jamiyar tasu?

Niger's Prime Minister Brigi Rafini (L) in the capital Tripoli on May 5, 2012. AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA (Photo credit should read MAHMUD TURKIA/AFP/GettyImages)
Firaministan Brigi Rafini na kokarin magance rikici siyasar NijarHoto: Getty Images

"Wallahi ko ma bakwai ne a bisa bakwai su ka tafi wanann ba baraka zai kawowa ba tun da kowa ya sani sai su sai matansu."

Bisa ga dukkanin alamu kauna ba ta kai ga yankewa ba a tsakanin jami'yyun biyu inda wasu rahotanni suka tabbatar da wata ganawa da aka yi tsakanin Hamma Amadou da shugaban kasa Mahamadou Issoufou a fadarsa. Yayin da a daya bangaren firaminista Briji Rafini ke ta faman safa da marwa a tsakanin mutanen biyu a kokarinsa na neman shawo kan matsalar tun wankin hula bai kai su ga dare ba.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe