1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta sa sabbin dokokin corona

Abdul-raheem Hassan
December 2, 2021

A wani mataki na yaki da annobar corona, gwamnatin Tarayya da na jihohi a Jamus sun cimma matsaya na haramtawa mutanen da ba su yi rigakafin cutar ba shiga shaguna da sauran wuraren shakatawa da taron jama'a.

https://p.dw.com/p/43kjG
Deutschland |  Bund-Ländertreffen zur Corona-Pandemie
Hoto: John Macdougall/AFP/ Pool/AP/picture alliance

Dokar da tuni ta fara aiki a wasu jihohin kasar, za a fadada ta zuwa ko ina ba tare da la'akari da yanayin girmar cutar ba, cikin sabbon dokokin da gwamnatin ta amince a wannan Alhamis, har da rufe gidajen rawa idan aka tabbatar da karuwar masu kamuwa da cutar a cewar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Yanzu haka dai majalisar dokokin Jamus na duba yuwar tilasta allurar rigakafin corona kan kowa da kowa daga watan Febrairu na shekarar 2022.