Ba da kananan basussuka don yaki da talauci | Zamantakewa | DW | 17.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ba da kananan basussuka don yaki da talauci

A daidai lokacin da duniya ke bikin yaki da talaucia duniya, shirin ba da basussuka ga masu karamin karfi a Nijar yana tasiri wajen yaki da talauci a kasar.

Yaki da talauci na daga cikin maradun karni na Majalisar Dinkin Duniya, kuma tun lokacin da aka kaddamar da wannan shiri a shekarun baya, kasashe da dama sun gabatar da shirye-shirye da nufin kawar wa ko kuma rage yawan talauci a cikin kasashensu.

A jamhuriyar Nijar ga misali an gabatar da shirin ba da kananan basussuka ga masu karamin karfi don ba su damar yin sana'o'i iri daban daban da za su sama musu da kudaden shiga. A birnin Maradi dake zama cibiyar kasuwanci a jamhuriyar ta Nijar, an kaddamar da irin wannan shirin. Shin ko wane irin tasiri shirin na ba da kananan basussuka yake wajen rage radadin talauci a na birnin na Maradi?

Tallafi ga mata don yaki da talauci

Wakilinmu a Maradi Salisou Kaka ya rawaito cewa bincike ya nuna galibin matsalolin kuncin rayuwa da jama'a talakawa suke samun kansu a ciki na da alaka da talauci da rashin aiki. Wannan shi ya sa hukumomi a Nijar musamman ma Maradi suke tallafa wa mata da matasa ta hanyar ba su kananan basussuka domin dogaro da kai. Galibi kuwa wadanda aka ba wa irin wannan talafi sun yi nasara kamar dai yadda Madam Maryama Yawale Talari shugabar sashen bada kananan basussuka a birnin Maradi ta yi karin bayani tane cewa.

"Kungiyoyin mata 30 a da'irar Maradi muka ba wa wannan bashi. Tun wadanda muka ba wa bashi na fari mun ya yi musu amfani. Hanya babba da za ta fid da mata daga cikin talauci shi ne ba su bashi. Bisa basirarsu mata sun sa yadda za su sarrafa kudi ya haifar musu da riba."

An fara ganin alfanun shirin tallafin

Su kuma kungiyoyin farar hula sun yaba da wannan shiri suna masu cewa kwalliya ta fara mayar da kudin sabulu.

Madame Hasau Hajiya Indo dan Bawa na daya daga cikin matan da suka karbi wannan bashi, ta ce wannan bashin ya amfanesu, sun karu da shi suna samun abinci sakawa bakin salati da na biyan sauran bukatu da su da iyali. "Muna ci-gaba sosai."

Fata a nan dai shi ne wannan shirin ya bunkasa zuwa dukkan sassan kasar ta Nijar da ma sauran yankuna da ake fama da matsalar talauci.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin