Ba alamar cimma masalaha a cecekucen harkar gas tsakanin Rasha da Ukraine | Labarai | DW | 31.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba alamar cimma masalaha a cecekucen harkar gas tsakanin Rasha da Ukraine

Har yanzu ba wata alamar cimma daidaito a takaddamar da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha akan iskar gas jimn kadan gabanin cikar wa´adin da aka bayar. Jajiberen kowace sabuwar shekara dai kam hutu ne a Rasha, saboda haka babu wata alama a birnin Mosko cewar kasashen biyu na tattaunawa da nufin warware wannan takaddama. Kamfanin Gasprom na Rasha yayi barazanar katse tura iskar gas zuwa Ukraine daga gobe lahadi idan kasar ta Ukraine ta ki amincewa da karin farashin gas din. Gasprom ya na son ya ninka farashin gas din da yake sayarwa Ukraine har sau 4.