Ba Ƙofar Aljanna ba ce | Learning by Ear | DW | 18.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Ba Ƙofar Aljanna ba ce

default

Afirka nahiya ce mai kai da komo. Miliyoyin mutane kan bar gidajensu don neman aiki ko gudun yaƙe-yaƙe da faɗace-faɗace da kuma yunwa. Da yawa daga cikinsu kan yi tunanin samun wata kyakkyawar makoma a Turai. Shirin Ji Ka Ƙaru na ɗauke da cikakken labari.


Bobby ɗaya ne daga cikin 'yan Afirka miliyan 17 da ƙungiyar ƙasa da ƙasa akan guje-gujen hijira ta ce suna kan ƙaura. Akasarinsu na ci gaba da zama ne a Afirka tare da fatan samun aikin yi a gonakin koko a yammacin Afirka ko kuma ɗaya daga cikin masana'antun Afirka ta Kudu.

Amma Bobby ya tsayar da shawarar yin hijira daga ƙasarsa ta Ghana zuwa Jamus. To sai dai kuma Jamus ba aljanna ba ce kamar yadda yayi zato. Akwai wahala wajen neman izinin zama da samun aikin da zai ba shi isasshen kuɗin shiga.

A cikin sabuwar salsalar shirinmu akan gudun hijira zamu tuntuɓi ‚yan gudun hijira daga sassa daban-daban na Afirka domin jin ta bakinsu kai tsaye. Mu ji irin hanyoyi masu haɗarin da suka bi don shigowa Turai. Zamu tattauna da wasu matasa 'yan Afirka su biyu waɗanda suka tsayar da shawarar komawa gida bayan shekaru da dama na wahala a Turai. Sai kuma wani labari mai ban mamaki a game da wani Bajamushe, wanda yayi ƙaura zuwa Uganda domin neman kyautata makomar rayuwarsa.

Sauti da bidiyo akan labarin