Baƙin haure na ci gaba da tsallakawa Turai | Labarai | DW | 14.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baƙin haure na ci gaba da tsallakawa Turai

Hukumomin Italiya sun ceto baƙin haure fiye da 600 daga kan teku

Mahukuntan ƙasar Italiya sun ceto baƙin haure kusan 650 cikin kwanakin da suka gabata daga kan teku, kamar da hukumomi suka tabbatar a wannan Talata.

Mahukuntan ƙasar ta Italiya sun ce an ceto kusan mutane 300 a kudu maso yammaci na Sicily, yayin da wasu kusan 220 kusa da gaban ruwan Porto Empedocle. Baƙin haure daga ƙasashen Afirka ta kuma yankin Gabas ta Tsakiya musamman Siriya da Zirin Gaza kan ɗauki kasadar tsallakawa zuwa nahiyar Turai ta kan teku, abin da ke haifar da asarar rayuka masu yawa. Daga farkon wannan shekara an yi imanin fiye da bakin haure 100,000 suka samu nasarar tsallaka zuwa nahiyar ta Turai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane