Baƙi ′yan ci rani na cikin matsala | Siyasa | DW | 18.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Baƙi 'yan ci rani na cikin matsala

A dai-dai lokacin da duniya ke bikin yancin baƙi yan cirani, masana sun bayyana irin matsaloli da baƙi ke fiskanta a duniya

Chinese woman talk business with local women at a shop in Lagos, Nigeria, June 16, 2007. Market stalls are just one of the most visible signs of China's massive penetration into African economies. The Asian giant _ a ready buyer of oil and other raw materials for more than a decade _ is also a major bidder on construction projects, a multi-million-dollar lender and a growing player in Africa's telecommunications and textile industries. (ddp images/AP Photo/Sunday Alamba)

Chinesische Kleinunternehmer in Afrika

Ranar 18 ga watan Disambar ko wace shekara rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin bikin ranar baƙi ta duniya da nufin yin nazari kan matsaloli da baki ke fuskanta, wanda ake gani a matsayin keta hakin bani Adama.

Kasashe da dama sun dauki wannan rana da muhimmanci inda suke gudanar da bukukuwa na musamman saboda irin gudumowar da baki suke bayar wa wajen bunkasa tattalain arzikin kasa da kuma harkokin yau da kullum.

Malam Muhammad Bello sarkin Arewa wani malami ne a sashin tarihi na jami'ar jihar Gombe, ya bayyana cewa bwannan ranar tana da matuƙar mahimmanci ga baƙi.

Bikin ranar wannan shekarar dai na zuwa a dai-dai lokacin da baki ke gamuwa da kalubale daga fuskoki da dama kama daga kora ko hana su wasu hakkoki ko da kuwa sun zauna tsawon lokaci a wannan wurare.

Stadt der Einwanderer Markt im Noailles. In dem Viertel nördlich des Hafens spürt man an allen Ecken, dass Marseille eine Stadt der Einwanderer ist. In Noailles leben die Migranten in zum Teil sehr herunter gekommenen Häusern aus dem 18. und 19. Jahrhundert. Der Markt ist fast komplett in arabischer Hand. Foto: Ralf Bosen/DW Aufgenommen in Marseille am 20.11.2012

Wasu yan ci rani da suke a Turai

Sabanin kasashen da suka ci gaba inda ake rungumar baki tare da basu hakkoki na musamman saboda irin gudumowar da suke bayarwa, a Tarayyar Najeriya abin ba haka yake ba, don kuwa duk irin gudumowar da bako zai bayar ba zai samu wasu hakkoki ba duk tsawon zaman sa a wurin kuwa.

Malam Muhammad Bello ya bada misalai da irin yadda baki ke fama da matsaloli a Najeriya abinda yace yana haifar da koma baya.

Wannan matsala da baki ke fuskanta a wani lokaci kan zama tashin hakali, wani lokaci har da zubar da jini musamman a wasu sassa na Tarayyar Najeriya.

Yanzu haka a Tarayyar Najeriya wani dan sashi ba zai iya zuwa wani sashin kasar ya zauna ya mallaki gida ko shago ba saboda kawai shi ba dan asalin wannan yanki bane, abida ake gani yana ci gaba da haifar da wagegen gibi tsakanin shiyyoyin kasar.

Schlagworte: Megacities, Lagos, Nigeria, Kleingewerbe, Schuhputzer Wann wurde das Bild gemacht?: 23.12.2009 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Mushin, Lagos/Nigeria Bei welcher Gelegenheit/in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen?: Schuhputzer bei der Arbeit im Wohnviertel Mushin, Lagos/Nigeria

Wani dan ci rani ke wankin takalmi a Lagos

Ko me haifar da wannan matsalar da a baya babu ita tambayar da na yiwa Malam Salihu Abdullahi kenan wani marubuci kuma mai fashin baki kan harkokin yau da kullum a tarayyar Najeriya. Inda yace matsala ce ta siyasa da shugabanni basu kai ga daukar matakin warwarewa ba.

Ana danganta karuwar wannan matsala da rashin aiwatar da dokoki da zasu tilasta magance wariya da ake nunawa baki inda masharhanta ke ganin matukar ba'a tsaurara dokokin ba, to kuwa baki za su ci gaba da zama cikin mawuyacin hali.

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Muhammad

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin