1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBelarus

An yi afuwa wa masu bore a Belarus

Abdourahamane Hassane
August 16, 2024

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya rattaba hannu kan wata doka da ta yi afuwa ga wasu mutane 30 da aka daure a gidan yari saboda zanga-zanga

https://p.dw.com/p/4jZKD
Alexander Lukashenko
Alexander Lukashenko Hoto: BelTA/TASS/picture alliance

 A cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaban kasar Belarus ta sanar da cewa an yafe wa mata 14 da maza 16 da aka samu da laifin dake da alaka da zanga-zanga, ba tare da bayyana sunayensu ba. Daga cikin wadanda aka sakin wasu suna fama da rashin lafiya wasu kuma tsofi ne, in ji shugaba Lukashenko, yana mai ba da tabbacin cewa duk sun gane laifinsu kuma sun tuba. A cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Viasna, kusan mutane 1,400 ne ake tsare da su a kasar Belarus saboda adawa da gwamnatin Alexander Lukashenko wanda ya kwashe shekaru 30 kan  karagar mulki.