1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a ajiye azumin Ramadan saboda Corona ba

Mahmud Yaya Azare MNA/AS
April 8, 2020

Malamai a jami'ar Azhar ta kasar Masar sun ce ba za a iya ajiye azumin watan Ramadan saboda Corona da ke ci gaba da yaduwa a duniya ba.

https://p.dw.com/p/3af28
Libyen Feuerpause Fastenbrechen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Makwanni biyu kafin fara azumin watan Ramadan, a kuma daidai lokacin da cutar Corona ke ci gaba da yaduwa, shehunan Maluman Musulunci a cibiyar binciken addinin Islama ta jami'ar Al-Azhar da ke Masar, sun yi nazari kan ko za a ba wa musulman duniya damar shan azumin bana, don riga-kafin kamuwa da cutar ta Corona, da ke bukatar shan ruwa akai-akai.

Bayan doguwar mahawara da tuntunbar kwararru kan bangarorin lafiya da na zamantakewa, gami da hada kan nassosin Alqur'ani da hadisan Ma'aiki S.A.W, babbar majalisar maluman ta ce babu wata hujja a likitance da za ta sanya musulmi shan ruwa don riga-kafin kamuwa da cutar corona.

Dr Amr Abdul-Azeez, kwararre kan cututtukan da suka danganci mura, ya kara tabbatar da cewa, matakan kariya daga kamuwa da cutar Corona, ba sa bukatar shan azumi muddin dai ba dama mutum na fama da wasu cututtukan na dabam ba.