1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sauya wa Aung San Suu Kyi mazauni

Ramatu Garba Baba
June 23, 2022

Gwamnatin da ta kwace mulki a kasar Myanmar ta sake wa hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi mazauni zuwa wani gidan yari mai tsananin tsaro.

https://p.dw.com/p/4D9fg
Aung San Suu Kyi | Protest für ihre Freilassung
Hoto: Philip Fong/AFP/Getty Images

Sabon rikicin siyasa ya kuma kunno kai bayan da masu rike da madafun ikon kasar ta Myanmar suka sake daukar matakin rugawa da hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi wani gidan yari mai tsananin tsaro da ke a yankin birnin Nay Pyi Taw.

Tun a Febrairun bara da kotun kasar ta yanke mata hukuncin daurin shekaru goma sha daya, aka yi wa Suu Kyi daurin talala a wani boyayyen wuri jim kadan da kifar da gwamnatinta da sojojin suka yi.

Ana tuhumar Suu Kyi da zarge-zarge da suka haura goma, kuma kowannensu na dauke da hukuncin zaman gidan yari na akalla shekara goma sha biyar muddun aka kamata da laifi, cikin laifukan da ake zarginta da aikatawa, har da zargin magudi a zaben kasar da kuma gallaza wa 'yan kabilar Rohingya, wadanda tsiraru ne a Myanmar.