AU ta yi Allah Wadai da harin Somaliya | Labarai | DW | 29.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AU ta yi Allah Wadai da harin Somaliya

Babban jami'in Tarayyar Afrika a Somaliya Francisco Caetano Madeira ya soki mummunan harin da kungiyar al-Shabbab ta kai a birnin Baidoa a ranar lahadin nan.

Birnin dai na Baidoa wanda ke samun kulawar dakarun hadaka na rundunar Tarayyar Afrika kimanin dubu 22 mai suna AMISOM ya fuskani harin kungiyar ta al-Shabbab ne a ranar lahadi nan. A inda mutane kimamin 30 suka hallaka a yayin da wasu 61 suka samu raunuka daban-daban.

A nasa bangaren gwamnan birnin Abdurashid Abdullahi ya ce, daga cikin wadanda suka sami raunuka, 15 suna nan cikin mawuyacin hali a inda ya kara da cewar harin ya faru akan cikin tsakiyar wani wajen hada-hadar harkoki ciki da mutane a birnin na Baidoa.

Tuni dai kungiyar ta Al-shabbab ta yi ikirarin cewar itace ke da alhakin harin na Somaliya.