AU ta nemi a warware rikicin Burundi | Labarai | DW | 16.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AU ta nemi a warware rikicin Burundi

Ƙungiyar kasashen Afirka ta AU ta ce rikicin da ake yi a ƙasar Burundi babbar barazana ne ce ga ƙasar da ma yankin Tsakiyar Afirka baki ɗaya.

A wata sanrawa da fidda dazu, shugabar AU ɗin Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce irin abubuwan da ke faruwa a Burundi a 'yan watannin da suka gabata babbar matsala ce da ke buƙatar warwareta cikin gaggawa.Ms. Zuma ta ce muddin ana son zaman lafiya to akwai bukatar yin amfani da hanyoyi na laluma wajen kawo ƙarshen rikicin siyasar kasar da kuma mutunta yarjejeniyar Arusha ta shekara ta 2000 da aka cimma.

Wannan na zuwa ne bayan da a jiya Asabar wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba a birnin Bujumbura su ka hallaka Kanal Jean Bikomagu da ke zaman jigo a rundunar sojin ƙasar.