AU ta ja kunnen Yahya Jammeh ya sauka. | Labarai | DW | 13.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AU ta ja kunnen Yahya Jammeh ya sauka.

Kwamitin tsaro da sasantawa na kungiyar gamaiyar Afirka ya yi kashedi ga Yahya Jammeh ya sauka ya mika mulki cikin girma da arziki.

AU Präsidentin Nkosazana Dlamini-Zuma Archiv 16.07.2012 (Simon Maina/AFP/Getty Images)

Shugabar kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma

Kungiyar gamaiyar Afirka AU a ranar Juma'ar nan ta yi kira ga shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya martaba sakamakon zaben da aka gudanar a watan da ya gabata ya sauka ya mika mulki cikin girma da arziki, tana mai yin kakkausar kashedi da abin da zai biyo baya idan matakinsa ya kai ga haifar da tarzoma.

Kwamitin tsaaro da sasantawa na kungiyar ta AU yace daga ranar 19 ga wannan watan kungiyar ba za ta amince da Yahya Jammeh a matsayin halastaccen shugaban kasar Gambiya ba.

Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye a zaben kafin daga baya ya sauya ra'ayi yana mai cewa ba zai mika mulki ga Adama Barrow ba.

A waje guda kuma tawagar kungiyar raya cigaban kasashen Afirka ta yamma ECOWAS karkashin jagorancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Banjul a yau Juma'a domin tattaunawa da Jammeh yayin da ake baiyana fargabar kwararar yan gudun hijira idan rikicin siyasa ya barke.