AU ta amince da kasuwanci mara shinge
March 21, 2018
Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewarkasashe 44 na nahiyar ne suka amince da yarjejeniyar ta kasuwanci mara shinge bayan tsawon shekaru shida ana kai ruwa rana a kan wannan batu, da ke da nufin kawo kasashen kungiyar 54 karkashin inuwa guda.
Kuma wajibi ne kowace kasa ta cire kashi 90 na harajin kayayyakinta, domin kawar da shingen da ke haifar da karan tsaye a fannin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, musamma jinkiri kan iyaka, kamar yadda ministar harkokin wajen Ruwanda mai masaukin baki, Louise Mushikiwabo ta nunar:
" Yarjejeniyar ba takarda ba ce kadai, ta na da tasirin tattali arziki ga yawan al'ummar Afirka. Zai bude damar kasuwanci ga sama da mutane biliyan daya, wanda zai kawo bunkasar arziki a nahiyar, ta hanyar karuwar masu zuba jari , da fadada hanyoyin kasuwanci."
Sai dai yarjejeniyar za ta fara aiki ne kawai bayan dukkan kasashen sun amince a matakansu na kasa.