Asusun bunkasa tattalin arzikin EU
December 19, 2014Talla
Shugabannin sun amince da wannan sabuwar dokar ne yayin taron da suka gudanar a Brussels. Ko da yake shugaban kungiyar ta EU Donald Tusk bai yi cikakken bayani kan yadda za a samar da kudaden cikin asusun zuba jarin ba yayin jawabin da ya yi a wani faifayen Video kan dokar, rahotanni sun tabbatar da cewa za a kaddamar da asusun a shekara mai kamawa ta 2015, inda za a fara shi da kudi kimanin Euro biliyan 21. Za dai a yi amfani da kudaden da aka tara a asusun wajen bunkasa samar da makamashi da bangaren sufuri da kuma ilimi da binciken fasaha.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu