1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asarar rayuka a yunkurin juyin mulki a Habasha

Mouhamadou Awal Balarabe
June 23, 2019

Babban Hafsan sojojin Habasha da gwamnan yankin Amhara sun mutu bayan da wasu sojoji suka harbesu a yunkurin juyin mulki da ya ci tura. Sai dai Firaminista Abiy Ahmad na fama da kalubale wajen aiwatar da sauye-sauye.

https://p.dw.com/p/3KwbK
Äthiopien  Seare Mekonnen
Hoto: Addis Abeba city mayor office

Yunkurin juyin mulkin ya gudana ne a Amhara, daya daga cikin yankuna tara da ke cin gashin kansu a Habasha, inda wasu sojojin kundumbala suka kai hari a zauren da manyan jami'an gwamnatin jihar ke gudanar da taro. Gwamnan yankin Ambachew Mekonnen da kuma wani babban jami'i sun ji mummunan rauni, lamarin da ya kaisu ga rasa rayukansu daga bisani. Shi kuwa hafsan hafsoshin sojin Habasha janar Seare Mekonnen ya gamu da ajalinsa bayan da dogarin da ke kare lafiyarsa ya harbeshi a gidansa da ke Addis Abeba babban birnin kasar. 

Firaminista Abiy Ahmed sanye da kakin soja ya fito ta kafar talabijin inda ya tabbatar da yunkurin na juyin mulkin tare da ta bayyana cewar dakarun da ke biyeyya ga gwamnati sun yi nasarar dakileshi. Firimiyan ya yi amfani da wannan dama wajen jadadda matsayin da 'yan Habasha na tabbatar da hadin kan kasa da kaunar juna.

Abiy Ahmed Äthiopien
Firaminista Abiy ya sanya kaki lokacin da ya bayyana yunkurin juyin mulkiHoto: picture-alliance/AP Photo

  Ya ce: "'Yan Habasha ba sa son gwamnati mai haddasa rikici da kashe mutane. Sun tabbatar da cewar suna da karfin kawar da 'yan kama karya tare da gudanar da gwagwarmayar assasa mulkin dimukaradiyya. A cikin shekarun da suka wuce, al'ummar Habasha sun yi magana da murya daya don nuna cewa ba za su yarda da gwamnatocin da ke da dabi'ar mulkin kama karya ba. "

Tuni aka riga aka kama dogarin da ke tsaron lafiyar janar Seare Mekonnen, yayin da ake ci gaba da farautar jami'in da ke kula da tsaron gwamnan yankin Amhara ruwa a jallo. Dama Asaminew Tsige da ake nema ya fito daga kurkuku be a shekara ta gabata bayan da aka kamashi bisa zargin irin wannan yunkuri na juyin mulki a shekarar 2009.
      
Hanyoyin sadarwar na Intanet sun katse a kasar ta Habasha wanda ya sanya ba a samun cikakkun bayanai kan halin da ake ciki.  Amma sharhanta sun nunar nunar da cewa wannan yunkurin juyin mulki ya tabbatar da halin gaba kura baya siyaki da Firayiminista Habasha Abiy Ahmed ya shiga shekara guda bayan darewarsa kujerar mulki. Hasali ma sauye-sauyen da ya aiwatar a fannin siyasa da kuma fannin tattalin arziki suna cin karo da kalubale. Ko da watannin baya-bayannan sai da gwamnan mutane suka rasa rayukansu a fadace-fadacen kabilanci a wasu yankuna na kasar kan filayen noma da arzikin karkashin kasa.

Mohamed Nagash, edita a sashen Amharin na DW ya ce sauye-sauyen rundunar soji ne kawai zai sa firaministan gano bakin zaren warware rikicin da ake fama da shi inda ya ce :  "Abu ne mai cike da kalubale da sarkakiyar gaske. Da wuya a samu wanda zai iya cikakken bayani ko yin wani sharhi kan abin da ya faru, amma a bayyane take cewar wannan yunkurin juyin mulki abu ne da za a ce mai muni ne ga gwamnatin Abiy Ahmed. Abin da ya kamaci gwamnatinsa a yanzu dai shi ne ya yi duba a tsanaki tare da yin gyare-gyare ga rundunar sojin kasar don ta kasance karkashin ikonsa yadda ya kamata."
      

   Yankin Amhara da ke kan tsaunuka ya kasance mahaifar sarakuna da dama na kasar. Sannan kabilar Amhara ta kasance ta biyu mafi girma a Habasha bayan Oromo. Wadannan kabilun biyu ne suka kasance a sahun gaba shekaru biyun da suka gabata wajen gudanar da zanga zangar da ta yi sanadin faduwar gwamnatin tsohon Firaminista Hailemariam Desalegn. Sai dai wanda ya maye gurbinsa Abiy Ahmed wanda shi Oromo ne ya yi kokarin sakar wa 'yan adawa mara tare da bai wa kafofin watsa labarai 'yancin fadan albarkacin baki.

Äthiopien | Amhara Regionalregierung Büro für öffentlichen Dienst und Personalentwicklung
A hedikwatar gwamnatin Amhara ne aka fara yunkurin juyin mulkin na HabashaHoto: A. Mekonnen

Kasar Habasha ta kasance ta biyu mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, inda ta kunshi kimanin mutane miliyan 100, sannan tattalin arzikinta ya kasance mafi habaka a yankin gabashin Aifrka. Amma ta kasance daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya.