1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Artabun magoya bayan Bolsonaro da 'yan sandan Brazil

December 13, 2022

Tun bayan kayen da aka yi wa shugaba Bolsonaro mai barin gado a zaben da ya gabata, magoya bayansa da shi kansa ke nuna rashin amincewa da yadda zaben ya gudana, suna masu zargin magudi a zaben na Brazil.

https://p.dw.com/p/4Kr3l
Hoto: Adriano Machado/REUTERS

Jami'an tsaron Brazil sun yi taho-mugama da magoya bayan shugaba mai barin gado Jair Bolsonaro a kusa da shelkwatar 'yan sandan birnin Brasilia, inda masu boren suka cinna wuta tare da yin fito-na-fito da mahukunta.

Lamarin da ya faru a ranar Litinin ya biyo bayan umurnin kotu na tsare wani fitaccen magoyin bayan shugaba mai barin gado bisa zargin sa da yi wa salon mulkin dimukuradiyya barazana.

Hukumomi sun ce masu zanga-zangar sun yi kokarin kutsawa caji ofis na 'yan sanda domin fito da wanda ake tsare da shin. Daga nan a cewar 'yan sanda, suka fara artabu, har sai da suka yi amfani da barkonon tsohuwa da harsashin roba sannan suka iya tarwatsa masu zanga-zangar da suka rika yi wa jami'an tsaron ruwan duwatsu.