Artabu tsakanin Boko Haram da sojojin Kameru | Labarai | DW | 26.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Artabu tsakanin Boko Haram da sojojin Kameru

Wasu majiyoyin sojin kasar Kameru sun ce an yi dauki ba dadi tsakanin dakarun kasar da tsagerun kungiyar Boko Haram na Najeriya

Rahotanni na nuni da cewar tun a jiya Juma'a ce suka kai wasu hare-hare biyu cikin Kameru.

Lamarin ya yi sanadiyar hallaka akalla sojoji hudu, abin da ya janyo aka kara tura dakarun cikin yankin. Tuni kasar ta Kameru ta tura dakaru fiye da 1000 kan iyakarta da Najeriya, domin dakile hare-haren 'yan Boko Haram masu kaifin kishin addinin Islama, wadanda ake zargin suna neman kafa sansanonin tudun na tsira a Kameru. Wani jami'in soji ya tabbatar da faruwan lamarin a garin Bargaram, sai dai babu karin bayani.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita : Zainab Mohammed Abubakar