Arewacin Najeriya na fama da hare hare. | Labarai | DW | 13.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arewacin Najeriya na fama da hare hare.

Wasu 'yan bindiga sun halaka rayukan mutane a kananan hukumomi biyu na jihar Katsina ciki har da mai garin Faru, Dikko Usman, da ke karamar hukumar Matazu.

Haka kuma maharan sun kashe wasu mutane a garin 'Yan kara da ke karamar Hukumar Faskari duk dai a jihar ta Katsina.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma'a inda maharan suka kai hare-haren ta hanyar budewa mutane wuta.

Yunkurin wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba na tuntubar kakakin rundunar 'yan sadan jihar Katsina SP Isa Gambo ya ci tura, saboda bai amsa wayarsa ba.

Karuwar hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan Najeriyar ke ikirarin aniyar murkushe 'yan bindigar.