1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arcewar Boko Haram daga wasu garuruwa

Ubale MusaFebruary 2, 2015

Gwamnatin Najeriya ta ce ta sauya salon yaki kuma ta fara nasara da tallafin sojojin Chadin da ke kan iyakokin Najeriyar da Kamaru

https://p.dw.com/p/1EUgH
Nordkamerun Grenzregion zu Nigeria Soldaten Anti Terror
Hoto: AFP/Getty Images

Kasa da sa'o'i 24 da harin da aka kai birnin Maiduguri, gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce tana samun gagarumin nasara a sabon fadan da yanzu haka sojan kasar ke gwabzawa da taimakon makwabta. Ko bayan kare garin na Maiduguri da ma kwace motocin yaki kusan 20 dai gwamnatin tarrayar Najeriya da yammacin litini ta tabbatar da sake kwace garuruwan Mafa, da Gamboru Ngala, da Marte da Abadam da kuma Mallam Fatori a cikin jihar Borno.

A wani taron manema labaran da ta gudanar litini a Abuja dai, kakakin gwamnatin da ke kula da harkokin yaki da ta'addancin, ya kuma ce garuruwan Hong da Mubi ta Arewa da kudu, game kuma da Maiha da Michika da Shuwa da Woru Gyambi da Gombi da Vimtim da Uba da Bazza duk cikin jihar Adamawa dai sun ficce daga hannun yan kungiyar ta Boko Haram. Irin wannan nasara a jihar Yobe a cewar Mike Omeri dai ta faru a garuruwan Gujba da Gulani da suma suka koma karkashin ikon sojojin kasar a halin yanzu.

Alamun sauyin salon yakin dai ya faro ne tun bayan isowar sojojin kasar ta Chad zuwa kan iyakokin kasashen Najeriya da Kamaru mako daya bayan, abun kuma da ya kai ga jerin hare-hare kan 'ya'yan kungiyar ta ko'ina. Abun da ya sa ake ta'allaka nasarar da rawar sojan na Chadi dake dauke da jirage masu saukar Ungulu na yaki maimakon sojan Najeriyar dake kuka na rashi na makamai to sai dai kuma a fadar Omerin duk wata nasarar da Chadin ke iya ikirarin samu ta da hannu dama kafa ta najeriya na ragowar kasashen yankin tafkin Chad yanzu.

Nigeria Flüchtlinge in Maiduguri
Mutane da dama sun rasa matsugunnensu sakamakon Boko HaramHoto: picture alliance/AP Photo

Sama da 'yan ta'adda 500 ne dai kafafen yada labarai ciki da ma wajen Najeriyar suka ce sun kai ga asara ta rayuka sakamakon sabon yakin dake kara muni ga kasar da ke fiskantar zabe kasa da makonni biyun dake tafe. A yayin da a can a kasar kamarun ana nazarin irin fasalin da rundunar kasashen Africa mai wakilai 7500 zata kai ga kunsa domin tunkarar matsalar. To sai dai kuma a cikin gidan Najeriyar dai gwamnatin ta maida martani ga sabon harin da ya faru jim kadan da kamalla yakin neman zaben shugaban kasar a jihar Gombe.