Arangama tsakanin dakarun Isra′ila da Falasdinawa | Labarai | DW | 12.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arangama tsakanin dakarun Isra'ila da Falasdinawa

Mutane hudu sun sami rauni sakamakon fito na fito a tsakanin dakarun Isra'ila da Falasdinawa.

Dakarun Isra'ila wadanda ke rakiyar wasu Yahudawa zuwa wuraren ibada da sanyin safiyar wannan Alhamis, a wani wurin da ke yankin gabar tekun Jordan na Falasdinu, sun yi taho mu gama da Falasdinawa da ke yin zanga zanga, wanda kuma ya janyo raunata mutane hudu, kamar yadda majiyoyin kula da lafiya a Falasdinu suka sanar. Jami'an sun kara da cewar, wasu daga cikin wadanda suka sami raunin, an garzaya dasu ne zuwa wani asibitin da ke birnin Nablus, yayin da wasu kuma, dakarun Isra'ilar suka yi awon gaba dasu.

Dakarun tsaron Isra'ila dai suka ce sun bude wuta ne bayan da wasu Falasdinawa suka yi ta jifarsu da duwatsu. Sun kuma kara da cewar, suna rakiyar farare hula ne, wadanda basu tsokani kowa ba, amma daya daga cikin masu bore ya yayi harbi da wata karamar bindiga. Dama Yahudawa na zuwa ziyarar wani kabarin da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijirar Falasdinawa a yankin Balata da ke Nablus, inda a ke yawan samun tashe tashen hankula a tsakanin Falasdinawa da Isra'ila.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu