Aqmi ta ɗauki alhakin hare-haren Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aqmi ta ɗauki alhakin hare-haren Cote d'Ivoire

Mutane guda 14 suka rasa rayukansu yayin da wasu 22 suka jikkata a harin da wasu yan bindiga suka kai a Grand Bassam

Kungiyar Aqmi reshen Ƙungiyar Al-Qaida a yankin Magreb ta ɗauki alhakin kai harin da wasu 'yan bindigar guda shida suka kai a jiya a wani otel da ke a Grand Bassam a Kudancin Cote d'Ivoire.

Mutane guda 14 suka mutu akasari fararan hula a ciki har da wasu 'yan ƙasashen Faransa da Jamus da kuma Birtaniya da kuma wasu sojoji biyu yayin da wasau 22 suka jikkata.Wannan shi ne dai karo na uku da yan bindiga ke kai hare-haren na ta'addancin yammacin Afirka bayan Mali da Burkina Faso