AQIM ta ce ita ta kai hari a Mali | Labarai | DW | 06.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AQIM ta ce ita ta kai hari a Mali

Kungiyar AQIM da ke gwagwarmaya da makamai a Mali wadda ke da alaka da al-Qaida ta ce ita ce ke da alhakin kai harin da aka kai a tsakiya kasar ta Mali.

Harin da ya hallaka sojoji akalla takwas dai an bayyana shi da na farko da aka kai mafi kusanci da babban birnin kasar Bamako, tun bayan da Faransa ta jagoranci kai farmaki da ya fatattaki 'yan ta'addan a arewacin Malin kimanin shekaru biyun da suka gabata. Kamfanin dillancin labarai na kasar Moritaniya Al-Akhbar ya ruwaito mambobin kungiyar ta AQIM na cewa sun ma kwace iko da garin Nampala ba tare da shan wahala ba, kuma a yanzu haka sun kame wasu sojojin kasar ta Mali. Sai dai mai baiwa ma'aikatar tsaron Malin shawara Laftanar Kanal Diarran Kone ya ce a yanzu haka sojoji sun sake kwace iko da garin na Nampala.

Mawallafa:Salissou Issa/Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita:Umaru Aliyu