1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APGA ta lashe zabe a Anambra

November 10, 2021

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta baiyana dan takarar jam'iyyar APGA Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/42qEZ
Nigeria Präsidentschaftswahlen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Soludo wanda jam'iyarsa ta APGA ta shugabanci jihar na tsawon shekaru 16 ya sami nasara da gagarumar ratar kuru'u fiye da dubu daya kan abokin hammayarsa na jam'iya mai mulki ta APC Andy Uba.

Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Soludo murna, tare da bukatarsa da ya magance kalubalen da jiharsa da kuma yankin ke fuskanta.

Fiye da 'yan sanda dubu 30 ne dai aka tura jihar da ke zama guda daga cikin yankin da 'yan kungiyar IPOB ke rajin ballewa don kafa kasar Biafra. Da dama na ganin Soludo ka iya fuskantar kalubalen daga abokan hamayyarsa.