APC ta zabi janar Muhammadu Buhari | Labarai | DW | 11.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

APC ta zabi janar Muhammadu Buhari

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben fida gwani na takarar shugabancin kasar a karkashin laimar APC mai adawa.

Buhari dai ya kasance kan gaba da kuri'u dubu 3 da 430, yayin da gwamnan Kano Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ke mara masa baya da kuri'u 974 sai kuma tsohon mataimakin shugaban kasa a yayin mulkin Obasanjo Atiku Abubakar da ya samu kuri'u 954, sannan gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya samu kuri'u 624 yayin da Sam Nda-Isahiah na jaridar Leadership ya samu kuri'u 10.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu kuri'u 16 da basu da inganci daga cikin kuri'un da wakilai sama da 7000 suka kada. Ana iya cewa a yanzu dai ta tabbata cewa tsofon janar mai ritaya Muhammadu Buhari ne, zai fafata da shugaban kasar mai barin gado Goodluck Jonathan, da ke neman wani sabon wa'adin mulki na biyu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba