Anti-balaka ta yi harbe-harbe a Bouar | Labarai | DW | 07.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anti-balaka ta yi harbe-harbe a Bouar

Mayakan sa kai sun nemi turjewa bayan da aka nemi su mika makaman da suke aikata ta'asa da su a Bouar da ke yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mayakan sa kai na kungiyar Anti-balaba sun yi harbe-harben kan mai uwa da wabi a birnin Bouar da ke yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka Afirka ta Tsakiya sakamakon cafke wasu mambobinsu da aka yi domin kwance musu damarar yaki. Wata majiya ta soje da ba ta so a bayyana sunanta ba ta nunar da cewa rundunar sojojin Sangaris na Faransa ta harbe wani dan Anti-balaka daya a lokacin da ya ranta a na kare sa'ilin da ake neman kwace makaman da ke hannansa.

An ta jin karar bindigogi har i zuwa azahar a Bouar, inda bankuna da kasuwanni da kuma shaguna suka kasance a rufe. Su dai 'yan Anti-balaka suna farautar musulmin wannan gari sakamakon zarginsu da suke yi da hada kai da kungiyar tawaye ta Seleka. Sai dai garin na Bouar ya samu sararawa daga rikicin addini bayan da aka jibge Sojoji 450 na Faransa da na kasashen Afirka.

Sojojin Faransa sun ta shawagi da jirage masu saukar angulu a sararin samaniyar wannan gari domin samun nasarar kwace makaman da mayakan sa kai ke amfani da su wajen aikata ta'asa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu