1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ansar Dine ta tura wakilai a Burkina Faso da Aljeriya

November 3, 2012

Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da su ka mamaye arewacin Mali ta baiyana buƙatar tattaunawa da gwamnatin ƙasar.

https://p.dw.com/p/16cI2
Fighters from Islamist group Ansar Dine stand guard as they prepare to hand over a Swiss female hostage for transport by helicopter to neighboring Burkina Faso, at a designated rendezvous point in the desert outside Timbuktu, Mali Tuesday, April 24, 2012. Two main groups now appear to be competing to govern northern Mali: Ansar Dine, which wants to see Sharia law brought to Mali, and separatist rebels who already have declared an independent state. (Foto:AP/dapd)
Hoto: dapd

Ƙungiyar Ansar Dine, dake riƙe da wani yanki na arewacin ƙasar Mali ta aika tawagogi a ƙasashen Burkina Faso da Aljeriya, domin tattauna batun zaman lafiya a Mali.

Kungiyar ta ɗauki wannan mataki a yayin da gamayyar ƙasa da ƙasa ke shirye-shiryen tura runduna ta musamman, domin ƙwato yankin arewacin Mali da ƙungiyoyi masu tsatsauran kishin addinin Islama suka mamaye. Camma a watannin baya, Blaise Compaore da ƙungiyar ECOWAS ta ɗorawa yaunin shiga tsakanin rikicin ƙasar Mali, ya gana da tawagar Ansar Dine ba tare da cimma nasara ba.

Sai dai a yayin da take maida martani gwamnatin ƙasar Mali ta gitta sharruɗa guda biyu.

Hukumomin Bamako sun ce ba za su iya tattaunawa ba, game da matsayin Mali na dunƙulalliyar ƙasa, da kuma matsayinta na ƙasa inda kowa ke da 'yancin gudanar da addininsa.

Kungiyoyin Ansar Dine da MUJAO, sun ƙaddamar da shari'ar musulunci a yankunan da suka mamaye.

Ko da wannan sabuwar tattaunawa ta cimma nasara, gwamnatin Mali ta buƙaci a ci-gaba da shirin yaƙi domin fuskantar sauran ƙungiyoyi masu alaƙa da Alka'ida, waɗanda suka girka sansani a yankin Sahel da Sahara.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal