1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Safarar miyagun kwayoyi ya karu a lokacin Coronavirus

Ramatu Garba Baba
June 25, 2020

Ofishin yaki da shan miyagun kwayoyi da aikata muggan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya UNODC ya nemi matakan shawo kan matsalar durkushewar tattalin arzikin duniya don gudun jefa manoma cikin halin tasku.

https://p.dw.com/p/3eKND
Opiumproduktion
Hoto: dapd

Wasu sabbin bayanai da Ofishin yaki da shan miyagun kwayoyi da aikata muggan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya UNODC ya fitar, sun ce masu safarar miyagun kwayoyi na cin karensu ba babbaka a lokacin wannan annobar Coronavirus, akasarin ma'aikata a kasashe kamar Afganistan da wasu na yankin Latin Amurka sun tsinci kai a aikin gonaki da ake noma tabar Wiwi don samun kudade.


Rahoton ya gargadi gwamnatoci da su dauki matakan shawo kan matsalar durkushewar tattalin arzikin duniya don gudun jefa manoma cikin halin da ba su da zabi fiye su tsunduma noma harmatattun ganye irinsu tabar wiwi. Baya ga haka ma dai an gano alkaluman yawan masu ta'amalli da miyagun kwayoyin ya karu sosai tun bayan bullar annobar da ta sanya takaita zirga-zirga.