Angela Merkel za ta kai ziyara Faransa | Labarai | DW | 20.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel za ta kai ziyara Faransa

Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus tana zuwa ne yayin da aka cafke wani dan gudun hijira a Jamus bisa masaniya a kan abin da ya faru a Paris.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana shirin kai ziyara birnin Paris fadar gwamnatin kasar Faransa domin tattauna hanyoyin hadin kai bisa yaki da ta'addanci. Ofishin jakadancin kasar ya ce ranar Laraba mai zuwa Merkel za ta kai wannan ziyara.

Haka yana zuwa yayin da masu bincike na Jamus suka kama wani dan gudun hijira daga kasar Aljeriya, wanda ake zargi yana da masani kan hare-haren birnin Paris tun lokacin da ake kitsawa, kuma ya yi biris wajen shaida wa hukumomi. An kama dan gudun hijiran a garin Arnberg na Jihar Nord Rhine-Wesphalia. Kasar ta Jamus tana nuna yuwuwar samun 'yan gudun hijira fiye da 900,000 cikin wannan shekara.