Angela Merkel ta yi jawabi a Davos | Labarai | DW | 24.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel ta yi jawabi a Davos

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargaɗin cewar ya zama dole ƙasashen ƙungiyar Tarrayyar Turai su ci gaba da ƙaddamar da sauye sauye .

Donmin su kasance gogaggu akan gasar duniya ta ci gaban tattalin arziki ne, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana haka a taron tattalin arziiki dake gudana a birnin Davos na Switzerland.Ta sanar da cewar abin da ya kamata ne kawai a yi domin samun ci gaban nahiyar.

Ta ce ''A shekaru biyar da suka wucce babu wanda ya yi tunani cewa za mu iya rungumar dawamamen tsari domin kare darajar takardar kudin Euro. A yau ana cikin aiwatar da tsarin kuma abin ya yi kyau''.

Sannan kuma ta ce akwai barazana da ke ƙalubalantar ƙasashen Turai na rashi aikin yi ga jama'a galibinsu kuwa matasa.

Mawalafi : Abdourahamane Hasane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe