Angela Merkel ta gargaɗi shugaban Masar da ya tattauna da yan adawa | Labarai | DW | 30.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel ta gargaɗi shugaban Masar da ya tattauna da yan adawa

Shugabar ta baiyana haka ne a taron manema labarai na haɗin gwiwa da shugabannin biyu suka yi a birnin Berlin a ziyarar da Mohamed Mursi ke yi a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta buƙaci shugaban ƙasar Masar ɗin da ya soma tattaunawa da ƙungiyoyin yan adawa na ƙasar. a lokacin da ta ke yin magana Merkel.Ta ce'' ya kamata dukanin ɓangarorin yan siyasar ƙasar su ba da gudun mowar su wajan ganin a tabatar da kiyaye hakokin bil adama tare da samar da yancin yin walwalar na jama'a''

A cikin watan Disamba shekara bara ne, Jamus ta dakatar da shirin soke bashin da ta ke bin ƙasar ta Masar; wanda aka kiesta cewar kuɗaɗen zasu iya kai miliyion 250 saboda tashin hankali da ya yi kamarii a ƙasar.Mutane guda 54 suka rasa rayukan su a cikin yamutsin da aka soma a ƙasar tun a makon jiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi