Angela Merkel na ci-gaba da rangadin yankin GTT | Labarai | DW | 04.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel na ci-gaba da rangadin yankin GTT

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkerl ta isa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya inda zata tattauna da Sarki Abdullah. SG ta Jamus ta na rangadin kwanaki 4 ne a yankin GTT a wani yunkuri na farfado shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra´ila da Falasdinu da ya cije. Kafin ta bar birnin Alkahira, matakin farko na wannan rangadi na ta, Merkel ta shawarta da sakatare janar na kungiyar kasashen Larabawa Amr Moussa da shugaban Masar Hosni Mubarak. Merkel wadda kasar ta ke rike da shugabancin karba karba na KTT zata kuma kai ziyara daular hadaddiyar kasashen Larabawa da kuma kasar Kuwaiti.