1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar gwamnatin Jamus ta gana da takwaranta na Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
February 2, 2021

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna ta wayar tarho da shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou kan muhimman batutuwa da dama.

https://p.dw.com/p/3omgd
Niger Kanzlerin Merkel auf Afrikareise | Merkel und Präsident Issoufou
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Merkel wacce ta jinjinawa shugaban mai barin gado kan matsayinsa na kin sake tsayawa a zaben shugaban kasar da suka gabata, ta kuma jinjinawa gwamantinsa kan namijin kokari na shirya manyan zabukan kasar da suka hada da na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki zagayen farko.

Batun tsaro da ke addabar Nijar da ma yankin Sahel, hakan da na tattalin arziki na daga cikin wasu muhimman batutuwan da shuwagabannin suka tattauna a kai. Merker ta bayyana anniyarta ta tallafa wa Nijar ta kowane fanni musamman ma kan batun yaki da annobar corona.

Ko baya ga shugaban Nijar, Merkel ta kuma tattauna da firaministan Habasha Aby Ahmed ta wayar tarho kan batutuwa da dama ciki har da batun rikicin yankin Tigray da ya halaka fararen hula da dama.