Angela Mekel ta samu lamnar yabo | Labarai | DW | 17.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Mekel ta samu lamnar yabo

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta samu kyautar lambar ta Seoul, saboda matsayin da ta dage a kansa na yin Allah wadai da ta'asar da 'yan Nazi suka aikata a duniya

Kyautar ta yawan kuɗaɗe tsaba dala dubu dari biyu saboda amincewarta cewar Jamus na da hannu cikin ta'asar da gwamnatin 'yan Nazi ta Hitler ta aikata a duniya,na zaman wani babban ci gaba a gareta,.

Merkel ita ce mutun na 12 da ta samun wannan kyauta wacce aka fara ba da ta tun shekarun 1990. Alƙalan da suka tantanceta, sun ce a cikin jawaban da take yi, a kowane lokaci Merkel ta kan ambato aikin na asha da 'yan Nazi suka aikata tare da nuna takaicinta.