Andre Poggenburg na AFD ya yi marabus | Labarai | DW | 08.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Andre Poggenburg na AFD ya yi marabus

Wani jigo a cikin jam'iyyar masu kyamar baki ta AFD a Jamus Andre Poggenburg ya yi marabus, sakamakon zagin da ya yi a kan Turkawa haifafun Jamus a lokacin wani taron siyasa.

Andre Poggenburg dan shekaru 42 zai ajiye matsayinsa na shugaban 'yan majalisun na jam'iyyar AFD a Jihar Saxony Anhalt a karshen watan Maris. Ya ce zai yi  marabus din ne domin samun sauki ga irin matsin lambar da yake samu daga kafofin yadda labarai tun bayan da ya yi tabargarzar, jam'iyyarsa ta AFD ta soki lamirin furcin nasa, kafin ta bukaci ya yi marabus.