ANC na kan gaba a zaben Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 04.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ANC na kan gaba a zaben Afirka ta Kudu

Sai dai kuma jam'iyyar za ta iya rasa muhimman garuruwa kamar yadda sakamakon wucin gadin na zaben kananan hukumomin ya nunar.

Jam'iyyar ANC ta Jacob Zuma na kan gaba a sakamakon zabe na wucin gadi na kananan hukumomi da aka bayyana, wanda aka gudanar a jiya.Sai dai masu aiko da rahotannin sun yi gargadin cewar jam'iyyar ta ANC za ta iya rasa wasu manyan garuruwa masu mahimmanci,abin da zai iya zama faduwa mafi girma da ba ta taba yi ba a zabubukan kasar tun lokacin da jam'iyyar ta samu mulki.Sakamakon wucin gadi na zaben na nuna cewar ANC na da kishi 52 cikin dari yayin da babbar jam'iyyar adawar kasar AD ke da kishi 31.