Ana zaman makoki a kasar Haiti | Labarai | DW | 18.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana zaman makoki a kasar Haiti

Al'umma a kasar Haiti ta kasance cikin makoki bayan da wasannin al'adu na Karneval da suke gudanar wa shekara-shekara ya gamu da wani hadari a birnin Port-au-Prince.

A kalla mutane 16 suka rasu bayan da wata mota da ke cikin jerin gwanon motocin a wasannin na karneval ta taba wata wayar lantarki, abun da ya janyo konewar mutane da dama yayin wannan buki. Dubunnan mutane ne dai suka hallara cikin juyayi, cikinsu har da shugaban kasar ta Haiti Michel Martelly, da mai dakinsa da Firaministan kasar Evans Paul, inda suka jagoranci wani jerin gwano na nuna juyayi a titunan da ake wannan wasa na karneval a wani mataki na tunawa da marigayan, inda aka ayyana kwanaki uku na zaman makoki a fadin kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu