Ana zaman makoki a Jamhuriyar Nijar | Labarai | DW | 13.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana zaman makoki a Jamhuriyar Nijar

Hukumomi a Nijar sun ware kwanaki uku na zaman juyayin gomman sojojin kasar da 'yan ta'adda suka hallaka a hari da suka kai a kan iyakar kasar da Mali a makon da ya gabata.

A Jamhuriyar Nijar kwanaki hudu bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a wani barakin soji da ke yammacin kasar iyaka da Mali, hukumomi sun fitar da wani sabon adadi wanda ya runbunya na farko har sau uku.

Sanarwar mahukuntan ta tabbatar da mutuwar sojojin na Nijar 89 wata guda bayan harin Inates da ya hallaka wasu sojojin 71.

A halin yanzu dai gwamnatin ta Nijar ta kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar domin juyayin rashin mayakan da aka yi.

A ranar Lahadi ne dai gwamnatin ta Nijar ta yi taron gaggawa na kwamitin tsaro domin duba abubuwan da suka wakana yayin harin na Chinedagore inda da farko sanarwar ofishin ministan tsaro ta ce mutane 25 ne suka mutu yayin da wasu shida suka samu raunuka.