Ana zaben yankuna a kasar Kamaru | Labarai | DW | 06.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana zaben yankuna a kasar Kamaru

Gwamnatin kasar Kamaru, na gudanar da zaben majalisun yankunta a karon farko a yau Lahadi. Yankunan Kamarun 10 ne dai ciki har da biyu da ke a yankin renon Ingila

Sama da shekaru 20 ne dai kundin tsarin mulkin ya bayar da damar zaben na yankuna, to sai dai a wannan karon ne ake iya cewa 'yan kasa za su gani.

A karshen shekarar da ta gabata ne, Shugaba Paul Biya, ya yi alkawarin zaben a kokarin kwantar da wutar rikicin ‘yan aware da ke ruruwa a yankin renon Ingila na kasar.

Manufar hakan kuwa shi ne domin bai wa yankin karin ikon mulki musamman ma a kan batutuwan da suka shafi al’umomin da ke zaune a cikinsa.

Sai dai kuma a bayyane yake, galibin mazauna yankin dai ba su da kwarin gwiwa a wannan zabe na yau.