1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zaben 'yan majalisa a Ruwanda

Yusuf Bala Nayaya
September 2, 2018

Ana kada kuri'a a zaben 'yan majalisa a Ruwanda. Zaben da ake tsammani jam'iyya mai mulki ta (RPF) za ta kwashe mafi akasari na kujerun majalisar.

https://p.dw.com/p/34BRZ
Warteschlangen bei den Wahlen in Ruanda
Hoto: picture-alliance/dpa

Za dai a dauki kwanaki uku ana yin wannan zabe na 'yan majalisa a mazabu 2,500 a wannan kasa ta Ruwanda da ke yankin gabashin Afirka.

Fiye da mutane miliyan bakwai ne suka yi rijista a kan wannan zabe na kujerun 'yan majalisa 80.

Kujeru 24 an ware su ga mata yayin da aka kebe kujeru biyu ga matasa, haka kuma an ware kujera guda ga masu bukata ta musamman.

Sama da 'yan takara 500 ne daga jam'iyyu biyar da kuma 'yan takara hudu masu zaman kansu ke neman wadannan kujeru. Sai dai masana a fannin siyasa a kasar na cewa jam'iyyar Shugaba Paul Kagame za ta kwashe akasarin kujerun majalisar. Kawo yanzu dai jam'iyyar ta RPF ita ke da kujeru 76.

A ranar 16 ga watan Satumba ne dai za a bayyana sakamako na karshe na zaben.