1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ilawa na zaben 'yan majalisa

Gazali Abdou Tasawa
April 9, 2019

Al'ummar Isra'ila na gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da zai kai ga samar da sabon shugaban gwamnati tsakanin firamnista mai barin gado Benjamin Netanyahu da Benny Gantz.

https://p.dw.com/p/3GUOR
Kombibild: Benny Gantz und Benjamin Netanjahu

Al'ummar kasar Isra'ila na can a wannan Talata tana kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokoki da zai kai ga samar da sabon shugaban gwamnati a kasar tsakanin 'yan takara biyu wato firamnista mai barin gado Benjamin Netanyahu mai shekaru 69, da babban abokin hamayyarsa Benny Gantz tsohon babban hafsan sojojin Isra'ilan dan shekaru 59.

 Rahotanni daga Isra'ilar na cewa an soma zaben tun da sanhin safiyar wannan Talata inda Isra'ilawa sama da miliyan shida za su zabi 'yan majalisar dokoki ta Knesset su 120. Za a rufe runfunan zabe a karfe 10 na daren yau wato karfe bakwai na yamma agogon JMT.  Yaron Zalel na daya daga cikin mutanen da suka fito kada kuri'ar tasu a birnin Kudus, ya kuma bayyana fatan samun sauyi:

"Na zo ne nan dan saboda diyana da gyaran makomarsu. Lokaci ya yi na kawo karshen wannan mulki. kuma babu wani mutuman da ya gagara a maye gurbinsa"

Wannan zabe dai na zama zakaran gwajin dafin farin jinin Firamnista Netanyahu wanda ya share shekaru 13 kan karagar mulkin kasar da kuma ke neman wa'adin mulki a karo na biyar. 

Sakamakon wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a a karshen makon da ya gabata ya nunar da cewa 'yan takarar biyu za su yi kan-kan-kan, kuma da wuya wani ya iya samun cikakken rinjayen da zai ba shi damar yin mulki shi kadai ba tare da kulla wani kawance ba.