Ana zaben shugaban kasa a Madagaskar | Labarai | DW | 25.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana zaben shugaban kasa a Madagaskar

'Yan takara 33 ne ke fafatawa tsakaninsu da nufin darewa kan kujerar shugabancin kasar Madagaskar da ke fama da rikicin siyasa da koma bayan tattalin arziki.

A yau Juma'a ne al'ummar Madagaskar ke kada kuri'a zaben sabon shugaban kasa, da zai maye gurbin shugaba mai ci, wanda ya dare kan kujerar mulkin kasar shekaru hudun da suka gabata bayan da sojojin suka yi juyin mulki. 'Yan takara 33 wadanda dukkaninsu ba su taba rike wani babban mukami a kasar ba ne suke zawarcin wannan kujera mai alfarma.

Sai dai kuma manufofin biyu daga cikinsu na kama da juna a inda a lokacin yakin neman zaben da su ka gudanar, inda su ka yi alkawarin tayar da komadar tattalin arzikin kasar ta Madagaskar, idan suka yi nasarar zama shugaban kasa.

Shekaru da dama wannan tsibiri ya shafe ya na fama da rikici na siyasa da kuma karayar tattalin arziki. Bankin duniya ya nunar da cewa kashi 92 cikin 100 na al'ummar Madagaskar, na rayuwa ne da kasa da dala biyu na Amirka a kowace rana ta Allah.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman