1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaben majalisar dokokin tarayyar Jamus

September 22, 2013

Al'ummar Jamus na cigaba da kada kuri'a a zabukan majalisar dokokin kasar wanda zai share fagen fidda shugaban da zai jagoracin gwamnatin kasar nan gaba.

https://p.dw.com/p/19lqw
SPD-Kanzlerkandidat Peer Steinbrück (SPD) wirft am 22.09.2013 in einem Wahllokal in Bonn (Nordrhein-Westfalen) seinen Stimmzettel in die Wahlurne. Foto: Marius Becker/dpa ***FREI FÜR SOCIAL MEDIA***
Hoto: picture-alliance/dpa

An dai bude rumfunan zabe a fadin kasar da sanyin safiyar wannan Lahadi kuma za su kasance a bude har karfe hudu na yamma agogon GMT sannan ana sa ran fara fitar da sakamakon zaben da zarar an rufe rumfunan na zabe.

Kimanin Jamusawa miliyan 62 ne dai ake sa ran za su kada kuri'a a zaben da takara ta fi zafi tsakanin Angela Merkel ta jam'iyyar CDU wadda ke neman wa'adi na uku a matsayin shugabar gwamnatin kasar da kuma Peer Steinbrück na jam'iyyar SPD.

Tuni dai kuri'un jin ra'ayin jama'a da aka yi suka nuna cewar jam'iyyar ta CDU ta Merkel za ta samu rinjaye a zaben, sai dai tana cikin tsaka mai wuya wajen zabar jam'iyyar da za ta yi kawance da ita idan an zo kafa gwamnati.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal