1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu wasu sojoji da laifin aikata kisan jama'a a Kamaru

Abdourahamane Hassane
June 11, 2020

Rundunar sojojin Kamaru ta ce an tuhumi wasu sojojin guda uku da laifin aikata kisan jama'a a yankin arewacin kasar inda ake yin magana da harshen Ingilishi.

https://p.dw.com/p/3ddrV
Symbolbild | Soldaten | Kamerun
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Kakakin rundunar sojojin na Kamaru Cyrille Atonfack Guemo ya ce ana tsare da sojojin a gidan yari na soja na birnin Yaounde. An dai samu sojojin guda uku da laifin kashe farar fula 23 a ciki har da yara kankana guda goma a cikin watan Maris da ya gabata a Ngarbuh da ke a arewa maso yammacin Kamarun.