Ana tattaunawa a Burkina Faso | Labarai | DW | 05.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana tattaunawa a Burkina Faso

Shugabannin ƙasashen Najeriya da Senegal da kuma na Ghana na tattaunawa da Lt. Col. Isaac Yacouba Zida

Shugabannin guda uku waɗanda suka isa a birnin Ouagadougou na tattaunawa a asirce da mutumin wanda ya yi ikirarin kansa a matsayin shugaban gwamnatin ruƙon kwarya na ƙasar.

Bayan faɗuwar gamnatin Blaise Compaore a makon jiya wanda ya shafe shekaru 27 a kan karagar mulki.Shugabanin guda uku wato Macky Sall na Senegal da Goodluck Jonathan na Najeriya da kuma John Dramani Mahama na Ghana. Wanda shi ne shugaban Ƙungiyar ECOWAS. za su yi ƙoƙarin shawo kan shugaban riƙon na Burkina Faso da ya miƙa mulki ga hannun farar hulla.