Ana taron ministocin harkokin waje na OSCE | Labarai | DW | 08.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana taron ministocin harkokin waje na OSCE

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gargadi kasashen Turai da su yi hattara dangane da hadarin da ka iya biyo bayan karfafa karfin iko a gwamnatin tarayya da kuma tauye yancin siyasa. 

Kerry na bayani ne a taron ministocin harkokin waje na kasashe 57 da ke cikin kungiyar kawancen tsaro da hadin kai ta OSCE. Taron wanda Jamus ta karbi bakuncinsa na gudana ne a birnin Hamburg ya kuma kunshi kasashe tarayyar Turai da Amirka da Rasha da kuma wasu kasashe na Asia.

Kerry yace a wasu kasashe da dama na kungiyar ta OSCE ana samun karuwar mulkin danniya da tauye hakkin dan Adam dana yancin kafofin yada labarai.

A nasa tsokacin Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya jaddada muhimmancin kungiyar kawancen tsaron ta OSCE wajen magance rikice rikice, inda ya yi nuni da rawar da kungiyar ta taka wajen wanzar da zaman lafiya a Ukraine.

" Yace Jamus ta karbi ragamar kungiyar a yanayi mawuyaci, inda a cikin shekarar yace abubuwa sun tabarbare kama daga rikicin Siriya dana Yemen da Iraqi da kuma Libya sanan da Ukraine inda ake samu kwan gaba kwan bayan rikici a kasar."