Ana shirin yin zabe a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 28.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana shirin yin zabe a gabashin Ukraine

Rikicin Ukraine ya dauki sabon salo, biyo bayan zargin da Ukraine ta yi wa Rasha na neman sake haddasa fitina, sakamakon goyon bayan zabe a gabashin kasar da ta ke yi.

Wannan batun dai na zuwa ne bayan da aka ambato ministan harkokin kasashen ketare na Rashan Sergei Lavrov na cewa Moscow za ta amince da kuri'un da za a kada ranar biyu ga watan Nowamba mai zuwa a yankuna biyu na gabashi da ke karkashin ikon 'yan awaren Ukraine masu goyon bayan Rasha.

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen ketare na Ukraine din Yevhen Perebyinis ya ce matakin da Rashan ta dauka na amincewa da kada kuri'a da yankunan da ke kiran kansu Tarayyar Donetsk da Luhansk za su yi, zai kawo cikas a tattaunawar sulhun da ake yi tsakaninsu.

Su dai 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha da kuma mahukuntan Moscow sun dage kan cewa kada kuri'a a yankin na gabashin Ukraine na daya daga cikin abubuwan da aka amince da su yayin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Rasha da Ukraine da kuma 'yan awaren a birnin Minsk a watan Satumbar da ya gabata,

Mahukuntan Ukraine sun musanta wannan batu suna masu cewa Rashar na son sake haddasa musu fitina ne kawai. Tuni dai al'ummomin yankin na Donetsk da Luhansk suka himmantu wajen yin shirye-shiryen zabe.